Zaben Kogi: Yan takarar PDP 5 sun janyewa Wada

21
Idris Wada

Jamiyyar PDP ta fara tantance wakilanta daga kananan hukumomi 21 na jihar Kogi domin zaben fidda gwani da za’ayi .

Anasa ran sama da wakilai 2576 ne zasu shiga cikin zaben fidda gwani da za’ayi ranar Talata.

A yanzu haka dai, masu neman jam’iyar PDP ta tsaidasu takara su biyar sun janye ma tsohon gwamna Idris Wada. Wadanda suka janye din sun hada da Muhammed Tetes, Victor Adoji, Salihu Atawodi, Grace Iye Adejor, da kuma Emmanuel Omebije.

Gabriel Adaku, da ya daga cikin dattakan shiyyar Kogi ta gabas ne ya bayyan janyewar da mutanen sukayi ma Idris Wada yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Lokoja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + nineteen =