Kyamar Baki: Nijeriya za ta nemi Afrika ta Kudu ta biya diyya

40

A yayin da ake ci gaba da Allah wadai da rikicin nuna kyamar baki a Afrika ta Kudu, gwamnatin Nijeriya ta bayyana aniyarta na neman diyya ga Afrika ta Kudu bisa kisar ‘yan Nijeriya da akayi da kuma lalata masu dukiya a rikicin baya bayan nan na kyamar baki da ya faru a kasar Afrika ta Kudu.

‘Yan Nijeriya naci gaba da nuna bacin rai kan irin kiyayya da al’ummar Afrika ta Kudu ke nunawa baki, in da ko jiya a garin Legas sai da matasa suka kai farmaki a kantin shoprite da kuma kamfanin MTN wanda dukkansu mallakar kasar Afrika ta Kudu ne a wani mataki na maida martini akan kisan ‘yan Nijeriya da akayi a can kasar.

A yanzu dai hankula sun tashi, ran mahukunta y abaci bisa cigaba da salwantar rayuka sakamakon kisa na kyamar bai da ke ci gaba da karuwa a kasar Afrika ta Kudu. Ya zuwa yanzu dai, akalumma sun tabbatar da cewa an kashe ‘yan Nijeriya mutum 3 kuma wasu da dama an lalata masu shaguna tare da salwantar dukiyoyinsu.

Masu wasoso na kokarin shiga shagunan baki a Afrika ta Kudu

Tun daga shekarar 2008 zuwa yau, kasar Afrika ta Kudu tayi kaurin suna wajen nuna kyama da cin zarafin ‘yan kasahen waje da ke rayuwa a kasar ba gaira ba dalili. Hakan kuwa ba komai zai haifar ba illa matsala na diplomasiyya tsakanin mahukuntar kasar da sauran kasashen duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × four =