Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya mutu

16

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe wanda shine ya jagoranci kasar zuwa ta farkin ‘yanci Robert Mugabe ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

Shugaban kasar ta Zimbabwe Emernason Mnangwagwa ne ya bayyana mutuwar Mugabe a shafinsa na tuwita, inda ya nuna kaduwarsa kan mutuwar tsohon ubangidansa kuma ya bayyanashi a matsayin dan gwagwarmaya wanda ke son ganin kasarsa taci gaba tare da nahiyar Afrika.

Mugabe dai yayi fama da jinya tun daga watan Afrilu a wata asibiti da ke kasar Singapore kafin Allah ya dauki rayuwarsa a yau.

Robert Mugabe shine shugaban kasar Zimbabwe na farko baya ta samu ‘yancin kai. A shekarar 2017 ne sojoji suka kifar da gwamnatinsa bayan ya shafe shekau 37 yana mulkar kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen − 9 =