Birtaniya: An soke tashin jiragen sama na British Airways

27

Kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na British ya dakatar da tashin wasu daga cikin jiragensa bayan da ma’aikatansa suka tsunduma cikin yajin aiki a yau Litini.

Yajin aikin wanda shine mafi girma, kamar yadda kamafnin ya bayyana, ya faru ne bayan gazawar mahukunta kamafanin wajen warware batun Karin albashin matuka jiragen, wanda hakan ya sa suka tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani, kuma ake sa ran cigaban sa har zuwa gobe Talata.

A wata sanarwa da kamfanin ya aikawa abokan hurdansa, ya bukaci da kada suzo filin tashi da saukan jiragen domin kuwa ma’aikatansa sun tsunduwa cikin yajin aiki.

Kungiyar matuka jiragen dai sun kwase sama da wata 9 suna neman Karin albashi tare da inganta aikin nasu. Yajin aikin dai da aka fara a yau zai sanya matafiya su samu tsaiko wajen tafiye-tafiyensu a Birtaniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × five =