Rikicin Kabilanci: Rayuka 8 sun salwanta a Ebonyi

16

Wani rikicin kabilanci da ya faru a jihar Ebonyi yayi sanadiyar mutuwar mutane 8, inda wasu da dama suka samu raunuka.

Rundunar ‘yan sandar jihar ta Ebonyi ta tabbatar da mutuwar mutane 8 a rikicin wanda ake zargin maharan sunkai daga kauyen Agila na jihar Benue.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Loveth Odah ta shaidawa manaima labarai cewa kwamishinan ‘yan sandar jihar Ebonyi Awosola Awotinde, manyan jami’an ‘yan sanda da kuma shugabar karamar hukumar Ohaukwu sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru bayan samun labarin hargitsin.

Loveth ta kara da cewa, kwamishinan ya bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu da kuma gujewa kai harin ramuwar gayya a yayin da jami’ansa ke kokarin ganin zaman lafiya ya dawo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × two =