Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago zasu sake zama ranar 16 ga watan Satumba

45
Ngige da Wabba

Gwamanatin tarayyya da kungiyar kwadago zasu sake zama ranar 16 ga watan Satumba don cigaba da tattauna batun mafi karancin albashi.

Babban sakataren kungiyar JNPSNC wanda ke wakiltar kungiyar kwadagon Alade Lawal ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da kamfanin dillacin labarai a Legas, inda yace an sauya ranar ganawarne bias uzurin jami’an.

Kungiyar ta kwadago da gwamnatin tarayya sun kai ruwa rana kan batun amincewa da mafi karancin albashin wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 18 ga watan Aprilu na 2019.

Tattaunawa tsakanin gwamnati da kuniyar JNPSNC da ke wakiltar kungiyar kwadago domin gyara alabshin ma’aikata ya hadu da tsaiko saboda rashin cimma matsaya kan wasu banbance –banbance.

Shugaban kungiyar kwadago Ayuba Wabba ya shaidawa manema labarai cewa zasu goyi bayan dukkan matakin da kungiyar JNPSNC ta dauka akan mafi karancin albashi.

Tunda farko dai, gwamntin tarayya ta bukaci Karin kaso 9.5 ga ma’aikatan da ke mataki na 7 zuwa 14, da kuma Karin kaso 5 ga wadanda ke mataki na 15 zuwa 17, a yayinda kungiyar kwadago ke neman Karin kaso 30 ga ma’aikatan da ke mataki na 7 zuwa 14 da kuma Karin kaso 25 ga wadanda ke mataki na 15 zuwa 17.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × three =