Atiku da Buhari: Babu shaidar cewa hukumar zabe ta INEC ta tura sakamakon zabe zuwa wata na’ura, inji kotu

17
Buhari da Atiku

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a yau Laraba tace babu wata shaida da ke nuna cewa hukumar zabe ta INEC ta tura sakamakon zaben shugaban kasa da akayi a wannan shekarar ta 2019 zuwa wata na’ura.

Da yake yanke hukuncin a madadin sauran alakalan, jagoran kotun mai shari’a Muhammad Garba yace masu shigar da karan, wato jam’iyar PDP da Atiku Abubakar sun gaza wajen tabbatar da cewa hukumar zaben ta na da na’urar da ta aike sakamakon zaben.

“ Nayi nazari sosai kuma na duba takarda 28 na zaben INEC wanda masu shigar da kara suka gabatar amma banga inda aka samar da wata na’ura don tura sakamakon zabe ba” inji mai shari’a Garba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + 8 =