Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kasar Indonesia Habibie ya rasu

21
BJ Habibie

Tsohon shugaban kasar Indonesia Bacharuddin Jusuf Habibie ya rasu a yau Laraba yana da shekara 83 bayan wata jinya da yayi na ciwon zuciya a asibitin sojoji na Jakarta.

Shugaban kasar Indonesia Widido ya mika sakon ta’aziyarsa zuwa ga al’umar kasar bias rasuwar Habibie.

“a madadin al’ummar Indonesia da gwamnati, ina mika sakon ta’aziya bias rasuwar farfesa BJ Habibie”

“Habibie kwararren masanin kimiyya ne kuma shine jagoran kawo sauye-sauyen fasaha a Indonesia kuma shugaban Indonesia na uku” inji Jako Widodo

A shekarar da ta gabata na 2008 ne aka kwantar da Habibie a asibitin Starnberg kusa da Munich na kasar Jamus inda akayi masa aiki a zuciyarsa.

Habibie, wanda masanin kere-kere ne, ya shugabanci kasar Indonesia a shekarar 1998 zuwa shekarar 1999.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × five =