Karin Haraji: Ta ina Talakan Nijeriya zai amfana?

45

Tun bayan da majalisar zartarwan Nijeriya tare da sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari suka amince da Karin kaso 7.2 daga kaso 5 na harajin da ake karba wajen ‘yan kasa, al’ummar Nijeriya suke ta tofa albarkacin bakinsu kan alfanu ko akasin hakan. Malam Haruna Bello da Hon. Abdulhamid Salisu Kanti sun bayyana abinda da talaka ya kamata ya sani game da ‘VAT’, dalilin yin Karin inda kuma suke tambayar ta ina talaka zai iya amafna da karin, duk dai a cikin wannan ra’ayin da suka rubuta. Asha karatu lafiya.

Kowace irin gwamnati na samun kudi ne akasari ta hanyoyi uku.

1.Biyan haraji, 

2.Ciyo bashi 

3. Siyar da ma’adanai 

Kamar Nijeriya ma’adanai da muke dashi har yake kawo mana kudin azo a gani shine danyen fetur. Yau an wayi gari idan muka siyar da danyen mai , bai Isa ya biya bukatun kasar ba, ballantana ayi ayyuka. 

‘VAT’ da ake karba, kashi 85% na zuwa jahohi da kananan hukumomi, a haka ana maganar jahohi da kyar ke iya rike Kansu saboda kudin dake shigo musu kusan sama da kashi 65 yana tafiya a biyan ma’aikata, yanzu idan aka ce su biya sabon albashi na dubu 30, tabbas da yawan su baza su iya biya ba, a wayi gari ana bautawa ma’aikatan gwamnati kadai wanda yawan su cikin al’umma bai wuce kashi 5 ba. 

Idan muka duba budget na 2019, dole sai da gwamnati ta ciwo bashi domin daukar nauyin manyan ayyuka, wanda a aikin titi kawai na Abuja-kano- da kuma akwanga- Jos-Gombe-Bauchi ya haura Naira Biliyan 500 banda sauran manyan ayyukan tituna a Arewa da kuma sauran yankunan kasar. 

A shirin inganta rayuwar al’umma kawai irin su ‘N-power’, ‘trader moni’ da sauran su shima wajen Biliyan 500 ne. Wanda ‘Tax’ zai taba jikin sa, shine wanda ke da manyan harkoki, kuma shima talaka zaiji a jikinsa domin kuwa farshin kayan masurufi zasu karu, yan kasuwa zasu fake da guzuma suna harbin karsana wajen karin kudin kayan miya, tattasai da dai sauransu. Allah ka tausaya ma kasar mu ta koma kan seti Ameen.

Akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa hakki ne akanta ta dinga yiwa al’ummar kasa cikekken bayani akan abubuwan da zasu shafesu kai tsaye, rashin bayani kan haifar da yaduwar maganganun da aka tsara ko aka shirya…

Al’ummar da sukafi damuwa da karanta rubutun Hausa suna da hakkin samun bayani, don anyi da turanci ba hakan ke nufin an fita hakkinsu ba.

Sannan afito da hanyoyi da talakan kasa zaiji sanyi a zuciyarsa ba abinda zai rika sosa masa zuciyar ba har yaji cewa kamar gwamnati na kun tatawa rayuwarsa,

Kullum abinda muke fadi bai kamata kasa irin Nijeriya mai cike da albarkatu, amma mafi yawan al’ummar dake cikinta suna kuka da talauci, amma kuma shuwagabannin dake jagorancin kasar sun zama attajirai su kaidai ke shanawa da dukiyar kasar.

Ya dai kamata ko ta hanyar rage yawan albashin da ‘yan majalisu da Sanatoci ke dauka ne talaka ya samu sassauci arage yawan albashin nasu yazama ba sai an rika ta6a talakan kasa ba. Domin kuwa babu ta inda karin zai amfanar da talaka, face sake jefashi cikin halin kunci.

Tsohon Shugaban Kasar Uruguay Joe Mujica ya isa ya zama abin misali ga shugabannin mu na Nigeria, saboda yana daga cikin shugabanni masu yaki da cin hanci da rashawa,

Tsohon Shugaban na Uruguay ya sadaukar da kashi casa’in cikin dari na Albashinsa ga Kungiyoyi masu zaman kansu da kuma marasa galihu yayin da kuma yake kwana a gidan gonar matarsa saboda rashin nisan dake tsakanin ofishinsa da gidan gonar,

Har ila yau Jose Mujica ya zabi ya hau mota kirar Bosswerjer wanda ko Kansila a wannan kasa bazaka gani da irinta ba ballantana shugaban karamar hukuma, Gwamna ko Dan Majalisa da Sanata. Burin Mujica shine al’ummarsa suji dadi, kasarsa kuma tagyaru.

Ko shakka babu, Mujica abin koyi da kwaikwayo ne, musamman a kasa irin Nijeriya da Talaka ke rayuwa kasa da Dala daya.

Malam Haruna da Abdulhamid sun aiko da wannan ra’ayin ne daga Gusau.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 2 =