RUFE IYAKOKI: Laifin Gwamnati Ko Talaka?

41
Kanar Hameed Ali mai ritaya, shugaban hukumar hana fasa-kwauri

Daga Muhammad Lawal Gusau

La’akari da sabbin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ke kirkirowa domin farfadowar tattalin arzikin kasa, musamman ta hanyar noma tare da wadansu shiri na tallafa wa matasa domin su dogara da kansu.

Umarnin rufe iyakoki wato ‘border’ domin dakatar da shigowa da kayan abinci musamman shinkafa yana tasiri sosai ta haujin inganta kayan noma na cikin gida Najeriya. Akwai kunya kwarai da gaske kasa irin Najeriya mai yawan mutane kusan miliyan dari biyu ta zama wadansu kasashe ne zasu ciyar da ita.

Idan zamu iya tunawa kafin rufe ‘border’, gwamnati ta baiwa manoman shinkafa tallafi na biliyoyin nairori wanda tallafin ya shafi manya da kananan manoma, tareda bada tallafi ga matasa domin kafa kamfanonin casar shinkafa na zamani.

A watannin baya babban bankin najeriya ta hanyar RIFAN wato ‘Rice farmers Association of Nigeria’ sun raba irin noma na shinkafa tareda injinin ruwa, takin zamani da dai sauran su ga alumma domin suyi noma, amma aka wayi gari mafi yawan wadanda suka amfana da wannan shirin suka sai kayan domin biyan wata bukata tasu.

Inada tabbacin da mutane sunyi amfani da wannan damar da bazamuyi kukan rufe ‘border’ ba, kuma idan muka lura yanzu duk manomin da yayi amfani da wannan tallafi ta hanyar da ta dace lallai zai dara.

Hasara ta biyu da mutane zasu fuskanta musamman wadanda suka zabi sayar da kayan da aka basu na tallafi ko bashi shine yana da matukar wahala su sake amfana da wani bashin daga babban bankin Najeriya muddin basu biya wancan ba. Da wannan nake baiwa manoma shawara akan amfani da kayan noman da suka karba tallafi ko bashi ta hanyar da tadace.

Daga karshe ina fatar duk wani tsari da gwamnati zata fito dashi yakasance tana sauraren ra’ayin alumma kafin aiwatar dashi.

Muhammad ya aiko da wannan ra’ayi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × four =