An rufe ofishin O’pay na Kano

25

Rundunar ‘yan sandan Najeriya shiyyar Kano ta rufe ofishin O’pay na Kano.

A wani samame da ‘yan sandan suka akai a ofishin na O’pay da ke titin lodge jiya Alhamis, sun umurci kowa da ya bar harabar wajen sannan kuma suka garkame ofishin.

Kamfanin O’pay dai yana amfani da baburan adaidaita sahu wajen jigilar fasinjoji a farashi mafi sauki inda ake biyansa kudi ta yanar gizo wato Internet.

‘Yan sanda sun bayyana cewa an basu umurnin rufe ofishin ne daga gwamnatin jihar Kano saboda kasa cika wasu ka’idoji da kamfanin O’pay din suka yi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 1 =