Gwamna El-Rufai ya sanya yaronsa a makarantar gwamnati

19
Gwamna El-Rufai sanda yakai Abubakar Al-Siddique makarantar Kaduna Capital

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanya yaronsa a makaranta gwamnati inda zai yi karatun primary.

Gwamnan wanda ya samu rakiyar mai dakinsa hajiya Ummi sun kai dansu mai suna Abubakar Al-Siddique zuwa makarantar Kaduna Capital dake Malali cikin garin Kaduna.

A baya dai gwamnan yayi alkawarin cewa indai yaronsa yakai shekara 6 zai sanya sa a makarantar gwamnati domin yayi karatu da sauran yara, kuma a yau Litini gwamna El-rufai ya cika alkawarin da ya dauka shekarun baya.

Gwamanan ya bayyana jin dadinsa saboda cika alkawarin da yayi, inda yace shima a baya makantar gwamnati yayi, duk kuwa da cewa bata kai nagartan wanda yaronsa ya shiga yanzu ba, amma dai yana alfahari da hakan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × five =