Yanzu-Yanzu: Kotu ta bada belin Sowore

14
Sowore

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umurnin sakin jagoran zanga-zangar #RevolutionNow Omoyele Sowore daga hannun jami’an tsaron DSS.

Alkalin kotun Taiwo Taiwo ya bada umurnin haka a cikin hukuncin da ya yanke yau Talata inda kuma ya umurci da a mika dan gwagwarmayan a hannun lauyansa Femi Falana (SAN) wanda shine zai rika kawosa kotu a duk lokacin kotu ke bukatarsa.

Tun da farko dai kotu taki sabuntawa hukumar DSS ikon cigaba da tsare Sowore, don haka lauyan nasa Femi Falana ya bukaci kotu da ta bada belin nasa batare da bata lokaci ba.

Alkalin kotun ya umurci Sowore da ya ajiye fasfo dinsa da sauran dukkan takardun tafiye-tafiyensa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 3 =