Aikin Hajji 2020: Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta fara yiwa maniyyata rijista

107

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano tace ta fara yiwa maniyyata aikin hajji na 2020 rijista. Sakataren hukumar Alhaji Abba Muhammad Danbatta ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai.

Danbatta ya nemi maniyyata da su fara biyan kudi naira 1,200,000 a matsayin kudin ajiya kafin hukumar aikin hajji ta kasa NAHCOM ta fitar da jadawalin kudin ko wace kujera da za’a biya a aikin hajji na shekarar 2020.

Sakataren hukumar jin dadin alhazan ya kara da cewa za’a yanke hukunci kan kudin da kowani maniyyaci zai biya da zaran hukumar aikin hajji ta kasa ta gama yin nazari akan yadda farshin dala zai kasance da kuma aikin da hidima da za’ayima mahajjata a garuruwan Madina da Makka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × one =