An rantsar da Biodun a matsayin Sanata mai wakiltar kudancin Ekiti

24
Biodun Olujimi

A yau Alhamis, an rantsar da Biodun Olujimi na jam’iyar PDP a matsayin sanata mai wakiltar kudancin Ekiti a majalisar dattawan Nijeriya.

Daukar rantsuwan nata yazo ne mako guda bayan kotun daukaka kara dake Kaduna ta soke zaben da akayima sanata Adedayo Adeyeye na jam’iyar APC.

Tun da farko dai, Biodun ta shigar da kara tana kalubalantar bayyana Adeyeye da hukumar INEC tayi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda tace ta samu kuri’u fiye da Adeyeye din.

A baya dai kotun sauraron kararrakin zabe da ke Ekiti ta soke zaben shi Adeyeye din bisa gamsuwa da hujjojin da mai karar ta gabatar, kuma ta bayyana Biodun a matsayin wacce tayi nasara a zaben watan Fabarairu na 2019.

Sai dai bayan daukaka kara da yayi a kotu, Sanata Adeyeye, wanda shine ke magana da yawun majalisar dattawa, yasha kaye a hukuncin da mai shari’a Anyanwu ya yanke a makon da ya gabata inda ya tabbatar da hukunci da kotun sauraron kararrakin zabe tayi na bayyana Sanata Biodun a matsayin wacce tayi nasara.

Biodun Olumiji dai ta samu kuri’u 54,894 yayin da abokin hamayyar nata Adeyeye ya samu kuri’u 52,242

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 1 =