Hadarin mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da raunata wasu mutane biyar a jihar Jigawa

75

Mummunar hadarin mota ya auku jiya Alhamis da misalin karfe biyu da rabi na dare, akan titin Hadejia zuwa Kano, kusa da kwanar Hadin, a yankin karamar hukumar Kaugama cikin jihar Jigawa.

Hadarin ya auku ne tsakanin wata karamar mota da ta fito daga Kafin Hausa da wata babbar mota da ta taho daga Kano.

Motocin guda biyu sunyi taho mu gama akan titin, inda babbar motar ta shiga jeji, yayin da karamar motar tayi raga-raga.

Karamar motar mai fentin taxi na dauke da fasinjoji 6 tare da direbansu, wanda anan take direban ya rasu. Wani fasinja guda shima ya rasu, sauran fasinjoji guda 5 kuma suka samu munanan raunaka da suka hada da karaya.

Wani direba wanda ya shaida lamarin, ya bayyanawa Sky Daily Hausa cewa ya tafi ya bar wadanda hatsarin ya shafa shanye a kasa, ana jiran zuwan jami’an tsaro. Kuma direban babbar motar ya tsira tare da motarsa lami lamiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − seven =