Hukumar JAMB tace ta shirya tsaf wajen kaddamar da binciken cibiyoyin rubuta jarabawar

8

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu JAMB tace ta shirya tsaf wajen kaddamar da binciken cibiyoyin rubuta jarabawar wadanda za a iya zabarsu wajen gudanar da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, ta shekara mai zuwa.

Shugaban sashen labarai na hukumar, Dr. Fabian Benjamin, shine ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai a Lagos.

A cewarsa, an kusa kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata, domin tabbatar da an gudanar da jarabawar kamar yadda ya kamata.

Kakakin na hukumar ya nesanta hukumar da rahotannin da wasu ke yadawa a kafafen labarai suna zargin cewa kokarin hukumar ta JAMB na binciken cibiyoyin yazo a kankanin lokaci, da mummunar aniyar hana wasu cibiyoyi samun damar gudanar da jarabawar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × four =