Titin Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi: Za a gana da Ministan Ayyuka

123

Sanadiyyar lalacewar titin Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi, wanda ya hada jihar Kano da jihoshi 4, al’ummar yankin sun yake shawarar aikawa da tawaga ta musamman domin ganawa da ministan ayyuka, Babantude Fashola, saboda neman agazawar gwamnati.

Alhaji Yunusa Haruna Kauyu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwarzo a majalisar dokokin jihar Kano, shine ya shaidawa manema labarai haka a Birnin Kano.

Yace tawagar zata hada da kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Alhaji Mu’azu Magaji, da sanatan da ke wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin-Maliya, da ‘yan majalisar wakilai na yankunan, da sauransu.

Titin na Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi, shine babban titin da ya hada jihar Kano da jihoshin Katsina, da Sokoto, da Zamfara da Kebbi, da ma wasu sassa na jamhuriyar Nijar.

An gina titin tun zamanin mulkin soja na shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida, amma ba a taba babban gyara akan titin ba, tun bayan da aka yi shi.

Dan majalisar yace gyaran hanyar gabadaya zai bunkasa harkokin walwala da tattalin arzikin jama’a a jihoshin guda 4.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × two =