‘Yansanda a Kano sun ceto wani yaro dan shekara 4 da aka sace

46

Rundunar ‘yansandan jihar Kano tace ta ceto wani yaro dan shekara 4 mai suna Abdulrahman Dalha, wanda aka sace shi a unguwar Zangon Rimi cikin yankin karamar hukumar Ungogo na jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da ceto yaron cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

A cewar Abdullahi Haruna, sun samu korafi ranar 10 ga watan Nuwamba a ofishin yansanda na Zango, dangane da lamarin, kuma wadanda suka sace yaron na neman kudin fansa na naira miliyan 4.

Yace take aka aika da tawagar dakile satar mutane na operation puff-adder tare da basu umarnin bibiya tare da kame masu garkuwar domin gurfanar dasu cikin awanni 24.

Yace jami’an sun bazama aiki inda suka kame babban mai laifin a unguwar Zangon Dakata yayinda yake shirin karbar kudin fansa.

Kakakin na ‘yansanda yace babban mai laifin, mai suna Anas Isa, dan shekaru 22, ya amsa laifinsa, inda ya jagoranci jami’an operation puff-adder zuwa gidan antinsa a kauyen Inusawa cikin karamar hukumar Ungogo, inda anan aka ceto yaron da aka sace.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 2 =