Gwamnatin Tarayya Za Ta Zuba Kudi Naira Miliyan Dubu 50 a Masana’antar Fasaha

25

Gwamnatin tarayya tayi aniyar zuba kudi Naira Miliyan Dubu 50 a masana’antar fasaha, a yunkurinta na ganin masana’antar ta tsaya da kafafuwanta, a cewar Ministan Labarai da Al’Adu, Alhaji Lai Mohammed.

Ministan ya bayyana hakan yayin bikin raba kyaututtuka ga mawakan Nahiyar Afirka, wanda aka gudanar a Hotel din Eko dake Victoria Island a Birnin Legos.

Lai Mohammed ya kuma ce gwamnati ta shirya wajen shigar da harkokin kasuwanci a masana’antar fasaha a Najeriya.

Ministan ya kuma ce da kokarin Ministan Sadarwa, gwamnatin zata tsaftace masana’antar tallace-tallace, domin tabbatar da cewa tallace-tallace na kaiwa ga wadanda aka yi niyya kuma ana tattara bayanansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 16 =