Shugaba Buhari Ya Bayar Da Umarnin Karasa Aikin Kamfanin Karafa Na Ajaokuta

16

Ministan Tama da Karafa, Mista Olamilekan Adegbite, yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ma’aikatarsa ta karasa aikin kamfanin karafa na Ajaokuta.

Olamilekan Adegbite ya bayyana haka ne a Abuja yayinda yake zantawa da manema labarai akan shirin bita kan ma’adanan kasa na Najeriya, wacce aka shirya yi ranar 2 ga watan gobe na Disamba.

Ministan wanda yayi magana ta bakin mai bashi shawara ta musamman, Mista Sunny Ekozin, yace ma’aikatar na aiki tukuru wajen tabbatar da umarnin shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimami ga gwamnati da mutanen kasashen Kenya da Jamhuriyar Demokradiyyar bisa iftila’in ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa suka yi mummunan ta’adi a wasu sassan kasashen.

Cikin wata sanarwa wacce kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya jiyo shugaban kasar na bayyana damuwa bisa asarar rayuka, da katsewar harkokin tattalin arziki da walwalar jama’a, da iftila’in ya haifar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − 4 =