Dakarun Sojin Iraqi Sun Harbe Masu Zanga-Zanga 14 A Birnin Kudancin Kasar Na Nasiriyya

22

Wasu majiyoyin ma’iakatan lafiya sunce dakarun sojin Iraqi sun harbe masu zanga-zanga 14 a birnin kudanci na Nasiriyya kuma mahukunta sun kafa dokar hana fita a birnin Najaf, bayan masu zanga-zanga sun kone ofishin jakadancin kasar Iran.

Sai dai, mahukunta sun kafa wata rundunar hadin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula domin kokarin dakile zanga-zangar.

Kone ofishin jakadancin na Najaf, wani birni mai tsarki a kudancin kasar, ya ta’azzara zanga-zangar a kasar ta Iraqi, bayan makonni ana zanga-zangar gama-gari da zummar kawo karshen gwamnatin da ake kallo a matsayin mai almundahana wacce ke samun goyan bayan fadar gwamnatin Iran dake Tehran.

Gazawar gwamnatin Iraqi da ‘yan siyasa wajen dakile zanga-zangar tare da biyawa masu zanga-zangar bukatunsu ne suke rura wutar kiyayya daga mutane.

Fira-Ministan kasar, Adel Abdul Mahdi, yayi alkawarin kawo sauye-sauyen zabe da yaki da rashawa, wadanda ba a jima da farawa sai jami’an tsaro suka kashe daruruwan masu zanga-zangar lumana a titunan birnin Bagadaza da biranen kudancin kasar.

Zanga-zangar wacce ta fara a birnin Bagadaza ranar 1 ga watan Okotoban da ya gabata, ta yadu zuwa sauran biranen kudancin kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 − 6 =