Za a kori malaman makarantar da basu da shaidar koyarwa zuwa ranar 31 ga watan Disamba

6

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin cewa dukkan malaman makarantar da basu da shaidar koyarwa a kore su daga makarantun zuwa ranar 31 ga watan gobe na Disamba, a cewar magatakardar hukumar yiwa malaman makaranta rijista a Najeriya, TRCN, Farfesa Segun Ajiboye.

Farfesan ya bayyana haka ne a Ibadan yayin yaye dalibai 200 wadanda suka karanci koyarwa a Jami’ar Ibadan.

A cewarsa, za ayi awon gaba da baragurban malaman da ke koyar da yaran Najeriya, tare da maye gurbinsu da kwararrun malamai wadanda ke da shaidar koyarwa, domin samar da nagartattun manyan gobe a kasarnan.

Magatakardar Hukumar yace dole malaman makaranta su tsaya kafada da kafada da sauran kungiyoyin kwararru a wannan zamanin da tattalin arziki ya dogara da ilimi.

Da yake jagorantar rantsar da sabbin malaman makarantar, Farfesa Ajiboye ya jaddada cewa duk malamin makarantar da aka kama da laifin karya dokar aiki, za a hukunta shi.

Ya kuma ce malaman Najeriya a yanzu suna da hanyar cigaban aikin su ta daban, sanadiyyar amincewar da majalisar ilimi ta kasa tayi akan hanyar cigaban aikin malaman makaranta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + ten =