Gwamnatin Jihar Kano za ta farfado da kwamitocin tsaftar muhalli

13

Gwamnatin Jihar Kano tana shirin farfado da kwamitocin tsaftar muhalli a fadin kananan hukumomi 44 na jihar domin karfafa dokokin tsaftar muhalli.

Shugaban kwamitin karta kwana kan tsaftar muhalli na jihar, Dr. Kabir Getso, shine ya bayyana haka bayan bibiyar aikin tsaftar muhalli na wata-wata da aka gudanar a birnin Kano.

Kabir Getso yace bisa la’akari da aikin tsaftar muhalli na watan Nuwamba, a bayyane take cewa akwai bukatar a wayarwa da mutane kai akan muhimmacin tsaftar muhalli.

A cewarsa, dabi’un dayawa daga cikin mazauna jihar yayin aikin, shi ya jawo bukatar farfado da kwamitocin a matakin mazabu da kananan hukumomi.

Shugaban kwamitin wanda kuma shine kwamishinan muhalli na jihar, ya bayyana takaici akan halayyar masu keke napep wadanda ke kauracewa bin dokar hana zirga-zirga yayin aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three − one =