Ministan Kimiyya Da Fasaha Yace Tattalin Arzikin Najeriya Yana Sauyawa

11

Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu, yace tattalin arzikin Najeriya yana sauyawa daga dogaro akan albarkatun kasa da kayan masarufi zuwa dogaro da ilimi da kere-kere.

Ogbonnaya Onu ya bayyana haka ne yayin bikin bayar da kyaututtuka ga mawaka na bana wanda makarantar Caleb ta shirya.

A cewarsa, kowace kasa a duniya, mai yawan jama’a ko akasin haka, ta samu cigaba ne saboda ta mayar da muhimmanci akan ilimi kuma ta fadada hanyoyin tattalin arzikinta.

Ogbonnaya Onu yayi nuni da cewa makarnatar ta Caleb tana da muhimmiyar rawar da zata taka wajen samar da ilimi nagari wanda zai bayar da dama ga kere-kere.

Ministan daga nan sai ya karfafawa dalibai da matasan Najeriya gwiwa da kada su damu da halin da Najeriya take ciki a yanzu, kasancewar kasar zata cigaba ta bunkasa kwanannan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 − two =