Yawan masu HIV ya ragu a Jihar Gombe

21

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya bayyana farincikinsa bisa raguwar yawan masu cutar HIV a jihar, daga kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2014, zuwa kashi 1.3 cikin 100 a wannan shekarar ta 2019.

Inuwa Yahaya ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Isma’ila Misilli, ya fitar, a wani bangare na sakon gwamnan na zagayowar ranar cuta mai karya garkuwar jiki a Gombe.

Gwamnan ya yabawa gudunmawar hukumar kula da cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar Gombe, bisa kokarin da take yi wajen dakile yaduwar cutar.

Gwamnan ya kuma godewa gudunmawar masu ruwa da tsaki daban-daban a yaki da cutar, musamman masu tallafawa da kudade da abokan aiki.

Yace sauran wadanda suka cancanci yabon sun hada da, kungiyoyin fararen hula, da shugabannin gargajiya da addinai, da ma’aikatan lafiya da ‘yan jaridu, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen + twenty =