Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta Kwace Manyan Motoci 7 Dauke da Giya

5

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kwace manyan motoci 7 dauke da giya, a wani sumame a titin Igbo Road zuwa Hausa Road a unguwar Sabon Gari.

Shugaban Hukumar, Sheikh Haruna Ibn-Sina, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim, ya rabawa manema labarai a Kano.

Haruna Ibn-Sina ya tabbatarwa da jama’ar jihar cewa hukumar baza tayi kasa a gwiwa ba a yakin da take da sayarwa da shan giya da sauran ayyukan alfasha a jihar.

Kwamandan yace gwamnatin jihar tayi doka tun a shekarar 2004 wacce ta hana sayarwa tare da shan giya da sauran kayan maye a jihar.

Ya kara da cewa duk wanda aka kama yana karya dokar, za a hukunta shi.

Haruna Ibn-Sina yace hukumar ta Hisbah ta kama mutane 6 yayin sumamen, wadanda ke da hannu wajen sayar da giyar da kula da shagunan shan giya a Sabon Gari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + 18 =