Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta rike adadin guraben alhazanta guda Dubu 95

4

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya tace ta rike adadin guraben alhazanta guda Dubu 95, domin maniyyatan hajjin badi.

Hukumar ta bayyana haka cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai ta hannun shugabar sashen hulda da jama’a, Hajiya Fatima Usara, a Abuja.

Fatima Usara tace an cimma matsayar hakan yayin sa hannu akan takardar fahimtar juna tsakanin karamin ministan harkokin waje na Najeriya, Zubairu Dada, da ministan harkokin Hajji da Umara na Saudiya, Saleh Benten.

Tace an sanya hannu akan yarjejeniyar ranar 5 ga watan Disamba, a shirye-shiryen hajjin badi.

Fatima Usara ta kuma jiyo ministan na aikawa da sakon shugaba Buhari zuwa ga gwamnatin Saudiyya, da ta taimakawa hukumar ta dukkan hanyar da zata iya, tare da taimaka mata wajen aikin jigilar alhazai zuwa kasar ta Saudiyya. A nasu bangaren, ministan Saudiyya, wanda ya jagorancin tawagar kasar wajen bikin sanya hannu akan yarjejeniyar, yace kasar Najeriya ta samu cigaba sosai a ayyukan Hajji da Umarah.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 1 =