Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo yayi tafiya zuwa Daular Larabawa

16

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yayi tafiya zuwa birnin Abu Dhabi a Daular Larabawa.

Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, yace mataimakin shugaban kasar zai yi jawabi a taron dabbaka zaman lafiya a kasashen musulmi karo na 6 wanda za a gudanar a gobe Litinin a Birnin Abu Dhabi.

A goben, mataimakin shugaban kasar zai gana da yarima mai jiran gado na masarautar Abu Dhabi, kuma mataimakin kwamandan sojojin Daular Larabawa, Sheikh Mohammed Al Nayan, a fadar shugaban kasa dake Abu Dhabi.

Shugabannin 2 zasu tattauna akan huldar kasashensu da kuma yadda za a cigaba da fadada huldar diplomasiyya da ta tattalin arziki tsakanin Najeriya da Daular Larabawa.

Ana sa ran dawowar mataimakin shugaban kasar a gobe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + 20 =