Shugaba Buhari Ya Yabawa Zakaran Damben Boksin Na Duniya Ajin Masu Nauyi Anthony Joshua

90

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa zakaran damben Boksin na duniya ajin masu nauyi, Anthony Joshua, bisa nasarar da ya samu kan Andy Ruiz dan kasar Mexico a daren jiya Asabar.

Mahaifiyar Anthony Joshua, Yeta da kuma mahaifinsa Robert Joshua ‘yan asalin Najeriya ne duk da cewa an haife shi ne a Watford ta kasar Ingila.

Shugaban Kasar cikin sakon taya murna wanda kakakinsa, Mista Femi Adesina ya fitar a Abuja, ya taya Anthony Joshua murna inda ya jinjina masa bisa farincikin da ya saka miliyoyin ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasarnan.

Anthony Joshua ya karbo kambunsa wanda Ruiz ya kwace daga hannunsa watanni 6 da suka gabata a Birnin New York na Kasar Amurka.

An gudanar da damben ne a Filin Wasa na Diriyah Arena a birnin Riyad na Saudiyya a gaban ‘yan kallo sama da 14,000.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 9 =