Shugaba Buhari Ya Bar Abuja Zuwa Kasar Egypt Domin Halartar Taro Akan Lalubo Hanyoyin Zaman Lafiya Da Cigaban Afirka

32

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa kasar Egypt domin halartar taro a birnin Aswan wanda aka shirya domin lalubo hanyoyin zaman lafiya da cigaba a Nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa shugaban kasar ya samu rakiyar gwamnoni, Ahmadu Fintiri na Adamawa da Godwin Obaseki na Edo da Mai Mala Buni na Yobe, kuma sun tashi daga sashen shugaban kasa na filin jiragen saman kasa da kasa na Nmandi Azikiwe dake Abuja, zuwa kasar ta Egypt, da misalin karfe 2 na rana.

Taron wanda za a gudanar daga gobe Laraba zuwa jibi Alhamis, an shirya shi ne domin tattaunawa akan alaka tsakanin zaman lafiya da cigaba a Nahiyar Afirka, tare da karfafa cigaban Afirka ta hanyar karfafa dokoki.

Sauran yan rakiyar shugaban kasa sun hada da ministan tsaro, Janar Bashir Magashi, da karamin ministan harkokin waje, Ambassada Zubairu Dada, da mai bawa shugaban kasa kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno, da shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ambassada Ahmed Abubakar.

Ana sa ran shugaban kasar zai dawo Abuja a ranar Juma’a.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 3 =