Mutane 6 ne Sun Mutu Yayin Hakar Ma’adanai a Jos

23

Mutane 6 ne suka mutu bayan wani ramin hakar ma’adanai ya rubza a kauyen Zawan cikin yankin karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Filato.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu a majalisar dokokin jihar Filato, Mista Gwottson Fom, shine ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a Jos.

Gwottson Fom yace shekarun mamatan sun kama daga 20 zuwa 27, inda ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne.

Manema labarai wadanda suka halarci wajen sun rawaito cewa mutane da dama sun samu raunuka sanadiyyar lamarin.

Dan majalisar yayi nuni da cewa wadanda suka rasun, suna hakar ma’adanai ne ta haramtacciyar hanya.

Tunda farko, wani shaidar gani da ido, Mista Emmanuel Gyang, kuma shugaban matasa a yankin, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya auku ne jiya talata da hantsi.

A cewarsa, sama da mutane 50 ne ke cikin ramin na hakar ma’adanai a lokacin da ya rubza a kansu, inda aka ceto sauran mutanen da raunuka daban-daban.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + 15 =