Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya Guda 9

10
Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya guda 9 a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Manema labarai sun rawaito cewa an rantsar da manyan sakatarorin a kashi 2, kafin a fara zaman majalisar zartarwa ta kasa.

Manyan sakatarorin guda 9 sun hada da Musa Hassan daga jihar Borno, sai Ahmed Aliyu daga jihar Neja, sai Olusola Idowu daga Jihar Ogun sai Andrew Adejoh, daga yankin Arewa maso tsakiya, da kuma Umar Tijjani daga yankin Arewa maso Gabas.

Sauran sune Dr. Nasir Gwarzo, daga yankin Arewa maso Yamma, da Nebeolisa Victor Anakali, daga yankin Kudu maso Gabas, sai Fashedemi Temitope Peter, daga yankin Kudu maso Yamma, da kuma Dr. Evelyn Ngige wacce take wakiltar yankin Kudu maso Kudu.

Jim kadan bayan rantsar da manyan sakatarorin, shugaban kasa da ministoci suka fara gudanar da taron majalisar zartawa na kasa na karshe a shekarar da muke ciki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =