Sojojin Sama Sun Lalata Wani Sansanin Yan Boko Haram a Borno

4

Hukumar Sojin Sama ta Najeriya tace dakarunta na Operation Lafiya Dole sun lalata wani sansanin yan Boko Haram dake Ngoske a yankin dajin Sambisa na jihar Borno.

Daraktan yada labarai na hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, shine ya bayyana haka a Abuja.

Yace an gudanar da aikine karkashin wani shirin yaki mai suna Operation Rattle Snake.

Shirin na operation rattle snake, wani shirine na sojin sama wanda yake kai farmaki a wasu gurare da aka ware a yankin Arewa maso Gabas, domin kara fatattakar sauran yan Boko Haram, tare da hana su sakewa.

An gudanar da aikin ne ranar 16 ga wata, bayan jirgin leken asirin hukumar sojin sama, yayin ayyukansa, ya gano wasu yan Boko Haram da suka taru a waje guda suna ayyukansu a sansanin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 5 =