Gwamnatin Tarayya Tace Kasar Najeriya Zata Fara Samar Da Kayan Injinan Masana’antu Da Na Jiragen Sama

12

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, yace kasar Najeriya na da ikon samar da kayan injinan masana’antu da na na jiragen sama, karkashin cibiyar cigaban ayyuka dake Enugu.

Onu ya fadi hakane a Enugu yayin kaddamar da ayyukan cibiyar.

Ministan yace abin alfaharine kasancewar cibiyar ta tashi tsaye wajen bayar da gudunmawa a bangaren fadada hanyoyin shigar kudade na gwamnatin tarayya.

Minstan ya bayyana farincikinsa bisa samar da aikin kira a cibiyar, wanda zai bayar da damar samar da kayan injinan masana’antu da na jiragen sama.

Yace da makerar guda 2, cibiyar zata iya samar da kayan karafuna wadanda suka hada da aluminium da kuma farin karfe.

A bangaren aikin samar da fensira na cibiyar, Onu yace ya gamsu kasancewar an samu fara aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 + nineteen =