Mafi Karancin Albashi: Gwamnonin Najeriya Sun Bukaci A Sake Bibiyar Yadda Ake Rabon Arzikin Kasa

13

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, yace har yanzu akwai bukatar sake bibiyar yadda ake rabon arzikin kasa, domin bayar da dama ga Gwamnoni su fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi na kasa.

Kayode Fayemi ya bayyana wannan matsayar yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya bayyana cewa bukatar sake bibiyar yadda ake kason da Gwamnoni ke yi, ya fara ne tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Gwamna ya bayyana cewa tuni har kungiyar ta mika matsayarta a kan yadda za a sake bibiyar yadda ake rabon arzikin ga hukumar kula da rabon arzikin kasa, domin dubawa.

Fayemi daga nan ya bayyana cewa Gwamnoni sun jajirce wajen biyan mafi karancin albashin, inda yayi alkawarin cewa babu jihar da zata biya kasa da naira dubu 30 kamar yadda aka amince.

Gwamnan sai dai ya bayyana cewa bai zama lallai karin albashin ya zama daidai ba tsakanin jihoshi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

7 + twelve =