Oshiomhole, Ya ki Amsar Kyautar Kirsimeti Daga Gwamnatin Jihar Edo

12

Shugaba na kasa na jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ki amsar kyautar kirsimeti daga gwamnatin jihar Edo.

Kakakin gwamnan jihar ta Edo, Mista Crusoe Osagie, ya bayyana haka cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a Benin.

Osagie yace kyautar kirsimeti ta musamman wacce aka warewa tsaffin gwamnonin jihar kuma aka aikawa Oshiomhole, an dawo da ita.

Yace an tura ‘yan aiken da gwamnatin jihar zuwa mika kyaututtukan a jajibirin kirsimeti.

Yace rabon kyautar kirsimeti aikin gwamnatin jihar ne na shekara-shekara wanda yake a matsayin hanyar nuna kauna, tare da inganta dangantakar zumunci tsakanin gwamnati da jama’a.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + one =