Kungiyar Kwadago Ta Kasa Ta Taya ‘Yan Najeriya Murna

6

Kungiyar kwadago ta ‘yan kasuwa ta kasa ta taya ‘yan Najeriya murna bisa jarumtarsu da juriyarsu tare da kishin kasa duk da kalubalen tattalin arzikin da kasar ta fuskanta a shekarar 2019.

Shugaban kungiyar, Mista Quadri Olaleye, ya jinjinawa ‘yan Najeriyan cikin wata sanarwa a wani bangare na sakonsa na sabuwar shekara.

Shugaban kungiyar ta kwadago ya bukaci gwamnati da ta fadada tattalin arziki, tare da rage kudaden tafiyar da gwamnati da kuma kaddamar da ayyukan da zasu inganta rayuwar mutane.

Ya kuma yabawa jihoshi bisa fara biyan mafi karancin albashi, inda yace hakan zai karawa ma’aikata kwarin gwiwa.

Olaleye ya kuma bukaci gwamnati da ta samar da karin ayyukan yi domin magance matsalar tsaro.

A cewarsa, anyi asarar rayuka dayawa sanadiyyar tabarbarewar tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + 1 =