Shugaba Buhari Ya Tabbatarwa Da Mutanen Kudu Maso Gabas Cewa Za Su Ga Abin Alkhairi Nan Ba Da Jimawa Ba

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da mutanen kudu maso gabas cewa za su ga abin alkhairi nan ba da jimawa ba.

Shugaban kasar yayi alkawarin cewa gwamnatinsa ta jajirce wajen gina yankin tare da samar da romon demokradiyya ga yankin na ‘yan kabilar Igbo.

Shugaba Buhari ya sanar da hakan a yankin karamar hukumar Bende na jihar Abia yayin kaddamarwa tare da mika aikin gyaran zaizayar kasa a Agbozu da kuma titin harabar cocin Methodist, inda anan kuma ya karyata rade-radin nuna wariya ga yankin na kudu maso gabas.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin karamin ministan ma’adanai da cigaban karafa, Uchechukwu Ogah.

Shugaba Buhari yayi alkawarin cewa gwamnati mai ci baza ta taba mayar da yankin na kudu maso gabas na ‘yan kabilar ta Igbo saniyar ware ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 + 16 =