Hukumar NECO Tace Ayi Watsi Da Labarin Cewa Tana Daukar Sabbin Ma’aikata

13

Hukumar jarabawar NECO ta bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da labarin cewa tana shirin daukar sabbin ma’aikata.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ta NECO, Mista Azeez Sani, ya fadi haka cikin wata sanarwa a Abuja.

Azeez Sani yace hukumar bata da aniyar daukar sabbin ma’aikata, inda yace labarin kanzon kurege ne aikin ‘yan damfara.

Azeez Sani ya kara da cewa, hukumar a karkashin shugabancin magatakardar hukumar mai rikon kwarya, Abubakar Gana, da kuma shugaban hukumar gudanarwa, Dr Abubakar Mohammed, suna kan tsarin next level na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yace hukumar ta dage wajen tabbatar da gaskiya da adalchi, tare da bin doka da oda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − nine =