Ministan Shari’ah Yace Gwamnatin Tarayya Tayi Daidai Wajen Tsare Omoyele Sowore Da Sambo Dasuki

7

Attoni Janar na kasa kuma Ministan Shari’ah, Abubakar Malami, yace gwamnatin tarayya tayi daidai wajen tsare Omoyele Sowore da Sambo Dasuki, tsohon mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, duk da umarnin kotu.

Abubakar Malami yace gwamnatin tarayya tana da damar tsare Sowore da Dasuki duk da umarnin kotuna na sakinsu saboda akwai wata karar da ke jiran sauraro a kotun koli.

Da yake magana a gidan talabijin na NTA, Malami ya dage akan cewa gwamnatin tarayya ba tayi kuskure ba, kasancewar har yanzu kotun kolin bata yanke hukunci kan karar dake gabanta ba.

Hukumar tsaro ta DSS ta tsare Sowore da Dasuki duk da umarnin kotuna daban-daban na a sake su.

Sai dai, a kwanakin baya, Abubakar Malami ya umarci hukumar ta DSS da ta saki Sowore tare da Dasuki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + 9 =