Shugaba Buhari Yayi Allah Wa Dai Da Kisan Mutane 19 Da Wasu Yan Bindiga Suka Yi A Jihar Kogi

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wa dai da kisan mutane 19 da wasu yan bindiga suka yi a kauyen Tawari cikin yankin karamar hukumar Kogi a jihar Kogi.

Shugaban kasar ya bayyana damuwar cikin wata sanarwar da kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya fitar a Abuja.

Daga nan ya shawarci al’ummar da rikicin ya shafa da su kauracewa kisan ramuwa tare da daukar doka a hannu domin dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Shugaban ya kara da cewa babu wata hujjar kisan mutanen da basu ji ba, basu gani ba, daga daidaikun mutane ko kungiya, bisa kowane irin dalili.

Shugaba Buhari yace kashe-kashe da kisan daukar fansa zai kara cigaban rikicin ne kuma hakan zai samar da rashin tsaro ga dukkan bangarorin.

Yace mutane su kauracewa daukar doka a hannu, saboda yin hakan zai kara lalata halin da ake ciki tare da yin kafar ungulu ga kokarin gwamnati na kawo karshen kalubalen tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − 10 =