‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 5 Sanadiyyar Fashewar Tukunyar Gas a Kaduna

13

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 5 sanadiyyar fashewar tukunyar Gas a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna a yammacin Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin a wata ganawa da yayi da manema labarai a Kaduna.

Yakubu Sabo ya kara da cewa wasu mutanan guda 4 sun samu munanan raunuka a lokacin da al’amarin ya faru bayan fashewar tukunyar Gas din a wani shago da ake dura iskar Gas.

Ya kara da cewa mutane guda biyu da al’amarun ya rutsa da su sun kone kurmus.

Haka kuma ya kara da cewa hadarin ya shafi wasu shagunan guda uku da ke kusa da shagon dura iskar Gas din, wadanda ke sayar da wasu abubuwan na daban.

Ya bayyana cewa mutane hudu da suka samu raunuka anyi gaggawar mika su zuwa asibitin Barau Dikko da ke Kaduna domin samun kulawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × four =