Rundunar ‘Yansandan Jihar Abia Ta Kame Mutane 5 Bisa Hannu A Sace Wani Yaro

2

Rundunar ‘yansandan jihar Abia ta tabbatar da kame mutane 5 bisa hannu a sace wani yaro daga Umuoba, helkwatar karamar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu a jihar.

Kwamishinan yansanda, Mista Ene Okon, ya tabbatar da kamen yayin da yake zantawa da manema labarai a Aba.

Ene Okon ya ce wadanda ake zargin sun kuma amince da laifinsu.

Yace wadanda ake zargin, wanda tawagar yansanda masu yaki da fashi da makami suka kama, suna cigaba da fuskantar bincike a halin yanzu.

Wata majiyar ‘yansanda mai tushe wacce ta nemi a sakaye sunanta ta shaidawa manema labarai cewa an kama wadanda ake zargin a jiya Litinin da safe a karamar hukumar Isiala Ngwa ta arewa.

Majiyar tace wadanda ake zargin sun fito daga garin Amaekpu na karamar hukumar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + eighteen =