Sabon Kwamishinan ‘Yansanda Umar Muri Ya Kama Aiki A Kaduna

8

Sabon kwamishinan ‘yansanda na jihar Kaduna, Umar Muri, ya kama aiki a Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa Umar Muri ya karbi aiki daga hannun Ali Janga, wanda aka shirya zai halarci makarantar manyan ma’aikata ta Kuru kusa Jos a jihar Filato.

A cewar Yakubu Sabo, sabon kwamishinan Umar Muri wanda shine kwamishinan yansanda na 38 a jihar Kaduna, dan asalin garin Muri ne a yankin karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Yana da digiri akan fannin shari’a daga jami’ar Maiduguri a jihar Borno, kuma ya halarci makarantar aikin shari’a ta Najeriya a jihar Lagos.

Yayi aiki na kankanin lokaci a matsayin mai bayar da shawara a harkar shari’a a hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, kafin daga bisani ya shiga aikin dansanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + 2 =