Gwamnatin Kaduna Tace Kotu Ce Ke Da Hurumin Yanke Hukunci Kan Zakzaky

8

Attoni Janar kuma kwamishiniyar shari’a ta jihar Kaduna, Aisha Dikko, tace kotu ce take da hurumin yanke hukunci ga shugaban kungiyar ‘yanuwa musulmi ta Shia, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kwamishinar ta kuma ce babu wani umarnin kotun dake zaman jira akan shari’ar Sheikh Zakzaky wanda gwamnatin jihar Kaduna ta shigar.

Aisha Dikko a cikin wata sanarwar da aka fitar a Kaduna, ta jaddada cewa bai kamata ake yayata shari’ar dake gudana ba, inda ta tabbatar da cewa gwamnati bata da niyyar janye karar da ta shigar akan Sheikh Zakzaky.

Ta kara da cewa gwamnati zata kyale kotu da zartar da hukuncinta akan shari’ar.

Attoni janar din tace Sheikh Zakzaky tare da matarsa Zinat, na fuskantar shari’a a babbar kotun jihar Kaduna, akan laifuffuka guda 8, cikinsu har da laifin kisan kai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 7 =