Kungiyar Malaman Jami’o’in Ta Ki Cewa Uffan Dangane Da Tattaunawarsu Da Buhari

5

Shugabanin kungiyar malaman jami’o’in kasarnan sun ki cewa uffan dangane da sakamakon zaman tattaunawarsu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugabancin kungiyar yana karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi.

Zaman tattaunawar ya zo ne bisa bukatar malaman jami’ar wadanda ke nuna turjiya dangane da shirin gwamnatin tarayya na shigar da su tsarin biyan albashi na IPPIS.

Shugaba Buhari ya umarci ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa da ta dakatar da biyan albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya cikinsu harda malaman jami’o’in tarayya, wadanda suka ki shiga tsarin albashin IPPIS kafin ranar 31 ga watan Oktoban 2019.

Daga baya gwamnatin ta kara yawan kwanakin zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban 2019.

Zaman wanda ya samu jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya samu halartar ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, da ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed.

Sauran sune ministan kwadago da samar da ayyuka, Dr. Chris Ngige, da kuma ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − nine =