Gwamnatin Jihar Borno Ta Fara Biyan Mafi Karancin Albashi Na Naira Dubu 30

5

Gwamnatin jihar Borno ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira Dubu 30 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Mista Bulama Abuso, ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Maiduguri.

Bulama Abuso yace gamayyar kungiyar kwadago a jihar ta yabawa gwamna Babagana Zulum na jihar, bisa cika alkawarinsa na cewa zai bayar da muhimmanci ga jin dadin ma’aikata.

Yace mafi karancin albashin da karin albashin anyi ga dukkan matakan aiki da albashi na musamman ga daukacin ma’aikatan jihar.

Daga nan sai ya bukaci dukkan ma’aikatan gwamnati da su saka abin alkhairin ta hanyar bayar sadaukar da kawunansu ga aiki, inda ya tabbatar musu da cewa za a duba dukkanin matsalolin da aka samu wajen fara biyan albashin.

Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Mallam Ali Goni wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana farincikinsa bayan ya karbi sabon albashinsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 12 =