Dakarun Sojin Najeriya Sun Dakile Kokarin Mayakan Boko Haram a Jihar Borno

12

Dakarun Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun dakile kokarin mayakan Boko Haram na kai hari zuwa wasu gurare masu raunin tsaro a jihar Borno.

Sojojin sun kuma cigaba da raunana mayakan na Boko Haram a arangama daban-daban a fadin Arewa Maso Gabas.

Kakakin ayyukan sojojin Najeriya, Kanal Aminu Iliyasu, ya bayyana haka a wata sanarwa.

Aminu Iliyasu ya jaddada jajircewar sojojin wajen dorewa da kokarin da suke yi har sai sun ga bayan dukkan ragowar mayakan Boko Haram da na ISIS.

Ya bayyana cewa dakarun bataliya ta 3 wadanda aka tura yankin karamar hukumar Gamborou-Ngala a jihar Borno a ranar 18 ga watan Janairu suka dakile wani harin ‘yan Boko Haram a garin Ngala.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 11 =