Shugaban Majalisar Dattawa Ya Raba Motocin Bus 34 Da Na Daukar Marasa Lafiya 4 a Mazabarsa

8

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya raba motocin bus 34 da na daukar marasa lafiya a asibiti guda 4 ga cibiyoyin lafiya a mazabarsa ta dan majalisar dattawa na Yobe ta Arewa.

Ahmad Lawan wanda ya kaddamar da rabon a Gashua, ya bayyana cewa an kashe Naira Miliyan 87 wajen samar da form na jarabawa shiga makarantun gaba da sakandire, JAMB, ga dalibai 200 wadanda ke neman gurbin karatu a manyan makarantu.

Ya kuma raba na’urar daidaita wutar lantarki, transformers, da kayayyakin koyon sana’a ga mutane 350, da famfunan banruwa ruwa da kayan noman rani, da komfutoci, da kekunan napep, da takin zamani, da injin buga iska da na malkade, tare da kuma jarin fara sana’o’i.

Ahmad Lawan yace ya kaddamar da shirin na koyar da sana’o’i ne domin samar da rayuwa mai inganci ga wadanda suka amfana.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamna Mai Mala Buni, ya yabawa shugaban sanatocin bisa abin alkhairin, inda yace hakan zai taimaka sosai wajen rage fatara da talauci a kananan hukumomi 6 dake mazabar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − four =